Babban Bankin Nijeriya wato CBN ta tabbatarewa da kungiyar manoman Auduga (NACOTAN) reshen jihar Ekiti cewa; za ta tallafa musu da kudi wajen ganin sun gudanar da noman auduga mai yawan gaske a jihar.
Wakilin Bankin CBN din, Mista Olutayo Sowumi, shi ne ya tabbatar da hakan a ranar Juma’a a yayin taron kaddamar da nasarar da aka samu na shirin noman Auduga na 2019/2020 a karkashin shirin Bankin CBN din da kuma kungiyar NACOTAN kan shirn ‘Anchor’s Borrower.’
Taron ya gudana ne a garin Itapaji Ekiti, dake karamar hukumar Ikole a jihar Ekiti. Sowumi ya ce shirin ‘Anchor’s Borrower’ gwamnatin tarayya ce ta kaddamar da shi domin bunkasa ayyukan noma da kuma rage talauci, ya ce bisa wannan dalilin ne CBN take son tallafawa membobin kungiyar manoman Auduga domin sauya rayuwarsu.