Rundunar Yan Sandar Jihar Katsina ta ce ta yi nasarar Chafke wasu mutane uku da suka kware wajen damfarar mutane wadanda suke bayyana a matsayin aljanu.
Kamar yadda Kakain Rundunar SP Gambo Isah ya ce mutane su ne Usman Adamu mai shekara 40 da Abba Ibrahim mai shekara 38 sai kuma Abdurrauf Iliyasu mai shekara 39.
SP Gambo ya ce dubun mutanen ya cika ne sa’in da suka kira wata mai suna Jamila Suleiman cewa su aljanu ne inda suka umarce ta da ta je bayan gari ta ajiye musu kudi naira dubu dari da hamsin ko kuma kuma su salwantar da rayuwar iyayen ta ko na yayan ta.
Tuni cikin figici ta yi amfani da umarnin nasu inda ta kai wannan kudi, kana dga bisani ta sake tura musu dubu chasa’in da bakwai zuwa asusun bankin aljanun kamar yadda suka yi ikiriari.
Rundunar har wa yau ta ce ta chafke wasu da ake zargi da fashin daji masu suna Hassan Magu mai shekara 20 da kuma Salisu Lado mai shekara 25 a ranar 17 ga watan Maris din wannan shekara.
Wadannan mutane da aka chafke an yi nasarar chafke su ne a hanyar su ta zuwa karamar Dandume don sake aika-aika.