Rahotanni sun nuna cewa kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta shirya bai wa mai tsaron bayan Ingila Dean Henderson Fam 170,000 duk mako a yunkurin da take yi na dauko dan wasan mai shekara 23, wanda ke zaman aro a Sheffield United domin ganin ya bar Manchester United kamar yadda rahoton Manchester Evening News ya labarto.
Henderson ana sa ran zai sake tafiya zaman aro har sai ya samu tabbaci daga Manchester United cewa za a ba shi damar fafatawa da David de Gea, mai shekara 29, wanda shi ne zabin farko na kungiyar Manchester United din.
A wani labarin kuma, Chelsea za ta yi yunkurin dauko golan Barcelona da Jamus Marc-Andre ter Stegen, mai shekara 28, kuma ta shirya bayar da dan wasan Sipaniya Kepa Arrizabalaga, mai shekara 25, a wani bangare na yarjejeniyar.