Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea da ke Ingila, ta lallasa takwararta ta Ingila wato Arsenal da ci 4 da 1 a wasan karshe na kofin Europa da aka buga a filin wasa na Baku. Tsohon dan wasan Arsenal din, wanda yanzu yake bugawa Chelsea wato Giroud shi ne ya fara zurawa Chelsea kwallo a minti na 49, a yayin da Pedro ya ci a minti na 60, sai Eden Harzard ya zura ta uku a bugun daga kai sai mai tsaron gida a minti na 65. A minti na 69 ne dan wasan Arsenal Iwobi ya zura kwallo daya, sai Hazard ya kara zura guda wacce ya maishe da wasan 4 da 1 a minti na 72. Wanda wannan a karshe ya bai wa Chelsea lashe kofin. Wasan dai ya gudana ne a daren jiya Laraba.