Cikin Bidiyo: Yadda Dan Kasar Indiya ya yi tattakin sama da kilomita 8,600 don isa Makkah domin Hajji
A watan Yunin shekarar 2022, Shihab Chottur daga Malappuram, Kerala ya fara tattaki zuwa Makkah, wanda yanzu ya kammala bayan shafe sama da shekara guda.
Ya zagaya kasashen Indiya da Pakistan da Iran da Kuwait domin Isa Makkah don gudanar da aikin hajjinsa.
Chottur ya shafe tafiyar sama da kilomita 8,600, bayan ya isa Makkah.
KARANTA WANNAN LABARIN: Girgizar Kasa Ta Afku A Birni Mafi Girma a Afirka Ta Kudu
Da yake tattara bayanan tafiyarsa a tasharsa ta Youtube, Chottur yace ya zagaya cikin jihohin Indiya har zuwa iyakar Wagah a Punjab, inda ya fuskanci koma baya kadan.
Mai gudanar da aikin Hajjin yana fuskantar matsalar bizarsa. Kotun koli ta ki amincewa da bukatarsa, amma bayan da yaje a kotun koli, ya yi nasarar shigar da karar da samun nasara.
Chottur ya ratsa kasar Saudiyya zuwa ta kasar Kuwait a mako na biyu na watan Mayun bana. A yanzu ya ziyarci Madina kuma ya yi tattaki zuwa Makkah da kafa, a cikin kwanaki 9 kacal.
Zai karasa kafarsa ta karshe bayan mahaifiyarsa ta tashi zuwa kasar Saudiyya.
A wani Labarin Kuma:An Kwashe Dubban Mutane Yayin Da Wani Dutse Ke Aman Wuta A Philippine
Dubban mutanen da ke zaune kusa da wani dutsen mai aman wuta a Philippine sun fake a cibiyoyin kwashe mutane.
Duwatsu masu tsananin zafi na fadowa daga Dutsen Mayon da ke tsakiyar lardin Albay.
Sama da mutane 12,800 ne aka kwashe zuwa wasu wurare masu tsaro don tsira da rayuwar su.
Dubban mutanen da ke zaune kusa da wani dutsen mai aman wuta a Philippine ne suka fake a cibiyoyin kwashe mutane yayin da jami’ai suka yi gargadin a ranar Lahadi game da hadarin lafiya daga toka da iskar gas mai guba da ke fitowa daga ramin wutar da ke tashi.
Masu bincike kan yanayin girgizar kasa sun ce sun sami labarin girgizar kasa akalla guda daya a cikin sa’o’i 24 da suka gabata kuma duwatsu masu zafi na fadowa daga Dutsen Mayon da ke tsakiyar lardin Albay.