- Gwamnatin Zamfara ta karyata ikirarin da tsohon gwamnan jihar Matawalle ya yi na cewa motocin da aka kwace a gidansa sayo su yayi daga Amurka.
- Tsohon Gwamna Bello Matawalle ya zargi Gwamna mai ci da jagorantar samamen zuwa gidansa wajen kama motocin.
- Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta sha alwashin ci gaba da kame wasu motoci da ake zargin tsohon Gwamnan ya sata.
Gwamnatin jihar Zamfara ta karyata ikirarin da tsohon gwamnan jihar, Bello Matawalle ya yi na cewa motocin da aka kwace a gidansa, wadanda ya sayo daga Amurka ne tun kafin ya zama Gwamna,Vanguard ta rawaito.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ‘yan sandan jihar Zamfara suka bayyana cewa, ya kamata tsohon gwamnan da ke fama da rikici ya fito da wasu takardu na motocin da ya ce nasa ne, kuma ya bar su aka kwato su.
KARANTA WANNAN: An Kwashe Dubban Mutane Yayin Da Wani Dutse Ke Aman Wuta A Philippine
Gwamnatin jihar Zamfara ta kuma ce an bi ka’ida kafin jami’an tsaro su je gidajen Matawalle; ya kuma yi watsi da zarginsa na cewa Gwamna Dauda Lawal Dare ya raka jami’an tsaro a lokacin da suka ziyarci gidansa.
”Zargi ne .Me ya hada Gwamnan Jihar Zamfara da aikin jami’an tsaro. Wannan ikirari bashi da tushe,” in ji wani babban mai taimaka wa Gwamnan.
Gwamnatin jihar ta nanata cewa kotun ta bada izinin ziyartar gidajen Matawalle inda aka kwace motoci 40.
Tsohon Gwamna Bello Matawalle ya zargi Gwamna mai ci da jagorantar samamen zuwa gidansa wajen kama motocin.
Matawalle ya kuma yi zargin cewa, baya ga motocin, jami’an tsaro sun hada da kayyakin matansa da suka hada da Hijabinsu, da wasu kayayyaki iri-iri da aka siya a shirye-shiryen daurin auren daya daga cikin ‘yan uwansa mata.
Da yake magana a wata hira da Sashen Hausa na BBC wanda aka sanyawa ido a ranar Lahadi, babban mai taimaka wa Gwamna Lawal Dare kan harkokin yada labarai, Mustapha Jafaru Kaura, ya ce jami’an tsaro ne kawai suka je gidajen tsohon Gwamnan bayan samun takardar izinin kotu.
Gwamnatin jihar ta dage cewa duk motocin da aka kwace daga gidajen tsohon Gwamna Matawalle; motocin Gwamnati ne.
Gwamnatin ta kuma yi watsi da ikirarin cewa motocin da aka kama na dauke da rubutun shugaba Tinubu ne.
Duk da cewa Matawalle ya ce adadin motocin da aka kama bai kai 40 ba, kuma yawancin motocin an sayo su ne daga Amurka, hukumomin jihar sun ce ‘yan sanda ne suka kirga motocin da aka kama.
Yayin da ya ke watsi da zargin cewa kwamishinan ‘yan sanda da gwamnan jihar Jafaru Kaura ne suka jagoranci aikin a gidajen Matawalle, ya ce “me Gwamna Dauda Lawal Dare zai yi a gidansa? Me ya shafi Gwamna Lawal Dare da motocin da aka kama?”
A halin da ake ciki kuma, Sashen Hausa na BBC ya rawaito cewa, rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta ce za ta ci gaba da kame wasu motoci da ake zargin tsohon Gwamnan ya sata.
A wani labarin kuma,Girgizar Kasa Ta Afku A Birni Mafi Girma a Afirka Ta Kudu
Girgizar kasa mai karfin awo 5.0 ta afku a birni mafi girma a Afirka ta Kudu
Girgizar kasar ta afku ne da misalin karfe 00:38 na dare agogon GMT mai zurfin kilomita 10.
Girgizar kasar ta akfu da sanyin safiyar ranara Lahadi