Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Gombe ta bayyana cewa tana sa ran samun ƙuri’u miliyan ɗaya a zaɓen gwamnan jihar na ranar 18 ga watan Maris, 2023.
Ayuba Aluke, kakakin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar na jihar, shine ya bayyana hakan a ranar Juma’a. Rahoton The Cable.
KU KARANTA KUMA: PSG na son ɗauko ɗan wasan Najeriya, Victor Osimhen
Aluke ya bayyana cewa jam’iyyar tana iya baƙin ƙoƙarin ta wajen ganin ta lashe zaɓen gwamna da na ƴan majalisun jihar da tazarar da ba a taɓa samu ba.
Ya ce nasarar da jam’iyyar ta samu a zaɓen ƴan majalisun tarayya na ranar 25 ga watan Fabrairu, inda ta samu kujerun ƴan majalisar wakilai biyar da sanatoci biyu ya nuna karɓuwar da jam’iyyar tayi a wajen mutanen jihar.
“Abinda PDP take harin samu ba wai nasara ba ce kawai, amma muna son muyi nasara da tazarar da ba a taɓa samu ba a jihar Gombe.” A cewar Aluke
“Muna sa ran samun ƙuri’u miliyan ɗaya, kuma da yardar Allah sai mun samu.”
“Al’umma sun san abinda PDP tayi kuma take kan yi a jihar wanda hakan ya bamu ƙwarin guiwar cewa nasara ta mu ce.”
Bayanan da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta saki, sun nuna cewa jihar Gombe tana da masu rajistar zaɓe mutum 1,575,794 wanda daga ciki mutum 1,534,954 suka karɓi katin zaɓen su.
NDIC Ta Bayyana Hanyoyin Kare Abokan huldar Bankuna Daga Masu Zamba
Hukumar inshorar ajiya ta Najeriya NDIC ta gargadi abokan huldar bankuna da sauran jama’a da su guji nuna bayanan bankunan su inda ta ce masu damfara suna kara yin kirkire-kirkire.
Hukumar NDIC a cikin gidan yanar gizon ta ranar Juma’a ta ba da shawarwari hudu ga abokan cinikin banki don kiyaye asusunsu daga ‘yan damfara.