By Abbas Yakubu Yaura
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, yace labarin cin zarafin yin lalata da satar bayanai da ke fitowa daga harabar jami’o’i da sauran manyan cibiyoyi Ilimi, sam ba za a amince da su ba.
Shugaban ya kuma bukaci kungiyoyin da ke jami’o’i da su hada kai don ganin an gyara wadannan matsalolin.
An ruwaito Buhari ya fadi haka ne a cikin sabuwar sanarwar da hukumar kula da jami’o’in Najeriya ta fitar.
An ce shugaban ya yi magana ne ta bakin wani daraktan hukumar Mista John Ahmadu a jami’ar tarayya da ke Oye-Ekiti ta jihar Ekiti.
An ambato shi yana cewa, “Labarin da ke fitowa daga wasu cibiyoyin mu, kamar cin zarafin yin lalata, cin zarafi, satar bayanai da sauran nau’o’in zamba da cin hanci da rashawa gaba daya ba za a amince da su ba.
“Kungiyoyi za su iya yin ƙari don taimakawa wajen magance waɗannan batutuwa don samun ingantaccen tsarin jami’a.
“Kudade wata babbar matsala ce da ke fuskantar tsarin jami’o’in Najeriya da kuma tushen farko na ayyukan masana’antu a cikin hasumiya na hauren giwa.
“Za mu ci gaba da tallafa wa tsarin jami’o’in ta hanyar inganta kudade da samar da ababen more rayuwa. Dangane da haka, gwamnatina ta sake mayar da hukumar ta TETFUND don samun damar magance matsalar ababen more rayuwa a manyan makarantunmu.”
Ya yi nuni da cewa a ko da yaushe gwamnatin sa ta mai da hankali sosai kan batun tallafin da jami’o’i ke bayarwa.
Sanarwar ta kara da cewa, “(Buhari), ya bayyana cewa ta fuskar raguwar albarkatun kasa a dukkan matakai, dole ne shugabannin jami’o’in su ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da gaskiya da rikon amana wajen tafiyar da albarkatun kasa.
Sannan “Ya umurce su da su zabo abubuwan da suka sa gaba a tsanake bisa isassun tsare-tsare da tanadin kasafin kudi, yana mai cewa, ikon samar da daidaito mai dorewa a tsakanin gajeru, matsakaita da kuma dogon lokaci na fifikon cibiya wata muhimmiyar alamace ta jagoranci na cigaba.