Jami’an tsaro na hukumar ‘Civil Defence’ ta bayyana cewa ta cafke wani saurayi da budurwa na aikata lalata a lungu a wannan wata na Ramadana bayan an sha ruwa.
Wannan lamari dai ya faru ne a Birnin Maiduguri, jihar Borno, inda Kwamandan rundunar ta jihar Borno, Abdullahi Ibrahim ya shaidawa manema labarai a jiya Juma’a.
Kwamandan ya bayyana cewa an kama matasan ne a ranar Talatar da ta gabata, 21 ga watan Mayu, a unguwar Abbaganaram
Kwamandan ya bayyana cewa wani dan agaji ne ya zo musu da rahoton cewa ga wani can yana lalata da wata a lungu, inda nan take jami’an Civil Difence suka dira a kansu suka kama su.
Matashin dai ya bayyana dalilinsa na yin lalata da budurwarsa a waje a matsayin cewa ba shi da kudin da zai iya kama dakin da zai kebe da budurwarsa kuma ga shi suna tsananin bukatar juna.
Za a gurfanar da saurayi da budurwar a gaban kotu da zarar an kammala bincike.