Majalisar wakilai na bincike kan Naira biliyan 186 da aka yi ikirarin kashewa a shirin ciyar da dalibai na Gwamnatin Tarayya daga shekarar 2016 zuwa yau. Majalisar ta bukaci bayanan ne a lokacin da babbar jami’ar shirin Sinkaye Temitope ta gurfana a gaban kwamitin bin diddigin kudade na majalisar a jiya Litinin.
A na ta jawabin, jami’ar ta ce shirin, wanda aka fara tun shekara ta 2016 kafin kafa Hukumar Jin-kai da Kai Agajin Gaggawa kuma a lokacin yake karkashin shirin tallafa wa marasa karfi na gwamnatin ya lakume kudi har Naira biliyan 186.
A cewarta, Naira biliyan 62 da miliyan 200 aka kashe a 2018, sai biliyan 32 da miliyan 200 a 2019, yayin da Naira biliyan 124 da miliyan 400 kuma aka kashe a shakarar da muke ciki ta 2020.
To sai dai yayin da yake mayar da martani, shugaban kwamitin bin diddigin, Oluwole Oke ya ce sam ‘yan majilisar ba su gamsu da yadda aka kashe kudaden ba. Kwamitin ya kuma bukaci a yi masa cikakken bayanin yadda aka kashe wasu Naira biliyan 64 daga cikin kudaden da aka kashe na ciyar da daliban.