Ma’aikatar lafiya ta jihar Filato ta shirya taron kwanaki uku ga ma’aikatan lafiya wadanda suka fito daga wurare biyar da aka tanada domin killace masu cutar Coronavirus, inda za a horas da su akan abin da ya shafi yadda ake kula da mai cutar Corona.
Da yake bude taron horaswar, Dr Nimkong Lar, Kwamishinan lafiya na jihar, ya ce manufar shi ne ilmantar da ma’aikatan lafiya dangane da cutar da yadda za a magance wannan muguwar cuta mai illatarwa.
A cewar Lar, taron horaswar zai kuma tallafawa ma’aikatan lafiya sanin ingantattun hanyoyin kariya daga cutar.