Masu Otel-Otel a jihar Legas sun koka saboda rashin ciniki sakamakon hauhawar cutar Coronavirus a jihar.
Manyan Otel a yankunan Somolu da Bariga dake jihar Legas, sun rurrufe Otel dinsu a yayin da kalilan ne ke bude wanda suma suke fuskantar karancin ciniki sakamakon ci gaba da garkame jihar da gwamnati ta bada umurni.