Cutar korona na ci gaba da yaduwa a sassan Nijeriya daban-daban, inda a ranar Lahadi a karon farko hukumar da ke yaki da cututtuka masu yaduwa ta ce cutar ta bulla a jihohin Kebbi da Taraba da Ebonyi da Bayelsa.
A jihar Taraba mutum shida aka tabbatar da sun kamu da cutar, kuma karon farko da cutar ta bulla a jihar. Sannan an samu mutum guda da ya kamu a jihohin Kebbi da Ebonyi da kuma Bayelsa.
Lokacin da yake sanar da bullar cutar a jiharsa, gwamnan Kebbi Abubakar Atiku Bagudu ya ce mutumin wanda ya kamu da cutar dan shekara 40 ne wanda ya yi balaguro zuwa Legas. Gwamnan ya tabbatar da cewa tuni aka killace shi bayan an gwada shi kuma an tabbatar yana dauke da cutar.
Ya zuwa yaznu jihohi hudu ne kawai cutar ba ta yadu ba a Nijeriya.