Duk da bazuwar cutar Korona a Nijeriya, inda ya zuwa yanzu mutum 1273 ke da cutar a Nijeriya, a yayin da 239 suka warke, 40 suka mutu sakamakon cutar, amma har yanzu cutar ba ta bulla a jihohi hudu na Nijeriya ba.
Cikin jihohin 36 da Nijeriya ke da shi, cutar ta bazu a jihohi 32 ciki harda birnin tarayya Abuja.
Jihohin da cutar ba ta bulla ba kuwa sune;
1. Kuros Ribas
2. Kogi
3. Nassarawa
4. Yobe