Hukumar da ke yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta Nijeriya, NCDC ta sanar da wanda ya kamu da cutar korona a karon farko a jihar Zamfara tun bayan sanar da kawo karshenta a jihar.
NCDC sun wallafa hakan ne a shafinsu na Twitter kamar yadda suka saba wallafawa a kowacce rana, inda suka bayyana jihar Zamafa da Kuros Ribas da Borno da Yone a matsayin jihohin da suka samu karin mutum daya.
Mutumin da ya kamu da cutar yana cikin karin sabbin mutum 653 da hukumar ta snaar a daren a Asabar da cewa suna dauke da wannan cuta. Sai dai a gefe guda kuma, hukumomin lafiya a jihar ta Zamfara sun nuna tababa kan wannan batu.