Da Ɗuminsa: An tsige Kakakin Majalisar Ogun, Oluomo
Kakakin majalisar dokokin jihar Ogun Kunle Oluomo an tsige shi.
Oluomo dai ya sha kaye a zarge-zargen da suka hada da zambar kudi zuwa rikicin shugabanci a majalisar dokokin jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN:Sanatocin Arewa: ‘Yan Majalisu 58 Sun Koka Kan Rashin Adalci A Kasafin Kudin 2024
Ta yiwu tsige shi ba zai rasa nasaba da yawancin zarge-zargen da ake yi masa ba.
A madadinsa, an nada Hon Oludaisi Elemide a matsayin sabon kakakin majalisar
A wani labarin kuma:Igbo ne za su tantance shugabancin ku kan yadda kuke tafiyar da Nnamdi Kanu – Ejimakor ga Tinubu
Aloy Ejimakor, mashawarci na cmusamman ga Nnamdi Kanu, shugaban masu fafutukar kafa kasar Biafra, IPOB, a ranar Talata ya bayyana yadda ‘yan kabilar Igbo za su ayyana matsayin shugaban kasa Bola Tinubu.
Ejimakor ya bayyana cewa ‘yan kabilar Igbo za su ayyana Tinubu ta yadda ya tafiyar da lamarin Kanu.