Yariman Wales, Prince Charles ya kamu da cutar Covid-19, mai Kula da Majalisar ya sanar da hakan a ranar Alhamis a shafin sa na Twitter.
“Da safe an gwada Yariman Wales, an samu ya kamu da cutar Covid-19, kuma a halin yanzu yana killace kansa,” inji sanarwar.
“A saboda hakan bazai samu damar halartar tarukan yau ba a Winchester, Kuma zai canja waya ranar nan bada jimawa ba.”
KARANTA WANNAN LABARIN: Da ɗuminsa: Ku dakatar da kamfanonin da aka samu da shigowa da gurɓataccen Man Fetur — Ƴan Majalisa ga NNPC
A wani Labarin kuma
An samu tada jijiyan wuya da ƙwanji a Majalisar Wakilai ta Ƙasa a zaman ta na ranar Alhamis, akan shigowa da gurɓataccen Man fetur a Najeriya.
Majalisar ta yanke hukuncin bincike akan lamarin, tana mai cewa dukkanin jami’an gwamnati da aka samu da laifin shigowa da rarraba man fetur ɗin, dole su fuskanci hukunci.
Kamfanin Man Fetur na Najeriya NNPC dana MRS Oil an ɗora masu tasowa alhaki akan lamarin.
Babban Manaja-Darakta na Hukumar NNPC Mele Kyari ya bayyana sunan Kamfanin Man Fetur na MRS da wasu guda uku akan laifin shigo da gurɓataccen Man Fetur a Najeriya.
Amma Kamfanin MRS a ranar Laraba ta musanta batun haɗa hannun ta shigowa da gurɓataccen man fetur ɗin, inda tace an hana shigowa dashi a Najeriya.