Hukumar gudanar da MTN sun sanar da rufe ofisoshin su a Nijeriya zuwa wani lokaci da ba su sanar ba. MTN sun bayyana hakan ne a wata sanarwa da suka fitar a ranar Laraba, inda suka ce sun samu labarin yadda aka kai su ofisoshinsu hari a garuruwan Legos, Ibadan da kuma Uyo. ]
MTN sun ce sun lura ofisoshinsu da ma’aikatansu sun zama ababen kai wa hari a wani harin ramuwar gayya bisa kashe ‘yan Nijeriya da ake yi a kasar Afrika ta Kudu. MTN sun ce a kokarinsu na ganin sun gudanar da ayyukansu, amma kare rayukan ma’aikatansu shi ya fi komai muhimmanci a yanzu. Suka ce da wannan suke sanar da rufe dukkanin ofisoshinsu a Nijeriya har zuwa wani lokaci.
MTN sun ce suna tir da dukkanin wani irin nau’in hare-hare na nuna warikar launi ko yanki. Kuma za su tabbata sun ci gaba da wanzar da zaman lafiya a Nijeriya da kuma sauran sassan Afrika.