Bayan mutuwar Sarauniya Elizabeth ta biyu, wacce ta fi dadewa a kan karagar mulki a tarihin Biritaniya, babban danta, Yarima Charles, ya zama sabon Sarkin Ingila. Kamar yadda jaridar DAILY POST ta ruwaito
Dimokuradiyya ta ruwaito cewa Sarauniya Elizabeth, wata alama ce ta biliyoyin mutane a duniya, ta mutu a yammacin yau Alhamis.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Sarauniyar Ingila Elizabeth Ta Rasu
A cewar sanarwar da Buckingham ta bayar ranar Alhamis, ta rasu tana da shekaru 96 a duniya, kuma fadar ya mata fatan Alheri.
Jaridar Guardian ta ruwaito cewa babban danta, Charles, mai shekaru 73, ya gaji sarauniyar a matsayin sabon sarki ba tare da bata lokaci ba.
A WANI LABARIN KUMA: Rikicin PDP: Murabus Din Da Jibrin Ya Yi A Matsayin Shugaban Bot Ya Bude Sabuwar Kofa – Shehu Sani
Sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya mayar da martani game da ci gaba da rikicin da ke faruwa a jam’iyyar PDP.
Sani ya ce murabus din Walid Jibrin a matsayin shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP, BoT, shugaban, ya bude sabuwar kofar rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar.