Hukumar DSS ta ce ta kwato kayayyakin da suka hada da na sojoji, da wasu makudan kudade iri daban-daban a gidan mai shiga tsakani da ‘yan fashi, Tukur Mamu.
Kakakin hukumar ta DSS, Peter Afunanya ne ya bayyana hakan a wani bincike da Daily Trust ta gudanar kan wani samame da aka kai a kan gidan dake Kaduna da ofishin Mamu da safiyar yau Alhamis.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rikicin PDP: Murabus Din Da Jibrin Ya Yi A Matsayin Shugaban Bot Ya Bude Sabuwar Kofa – Shehu Sani
Hukumar ta DSS ta ce abubuwa da dama da aka gano na da matukar tayar da hankali, inda ta ce za a gurfanar da mawallafin da aka kama a kotu.
“Ya zuwa yanzu, hukumomin tsaro da suka dace sun aiwatar da sahihin sammacin bincike a gidan Mamu da ofishinsa.”
“A yayin aiwatar da ayyukan, an kwato kayan cin zarafi da suka haɗa da kayan aikin soja.”
“Sauran abubuwa sun haɗa da adadi kudade iri daban-daban mai yawa da kuma kayan mu’amalar kuɗi. Yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike, tabbas Mamu zai samu rana a kotu,” in ji Afunanya.
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: Bayan Rasuwar Elizabeth, Yarima Charles Ya Dare Garagar Mulki
Bayan mutuwar Sarauniya Elizabeth ta biyu, wacce ta fi dadewa a kan karagar mulki a tarihin Biritaniya, babban danta, Yarima Charles, ya zama sabon Sarkin Ingila. Kamar yadda jaridar DAILY POST ta ruwaito
Dimokuradiyya ta ruwaito cewa Sarauniya Elizabeth, wata alama ce ta biliyoyin mutane a duniya, ta mutu a yammacin yau Alhamis.