Folajimi Mohammed, dan Ministan yada labarai da al’adu, ya rasa tikitin tsayawa takarar wakiltar mazabar Ikeja 1 a majalisar dokokin jihar Legas.
Dan Ministan wanda ke wakiltar mazabar a karo na biyu, ya kasa samun tikitin sake tsayawa takara a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC da aka gudanar a ranar Juma’a.
Yayin da Folajimi ya samu kuri’u tara a zaben,ya yinda abokin hamayyarsa, Seyi Lawal, ya samu kuri’u 15.
Magoya bayan Lawal sun yi ta murna yayin da shugaban kwamitin zaben, Comrade Ewuoso Olamide, ya ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.
A WANI LABARIN KUMA Injiniya Umar Abdullahi Ganduje wanda aka fi sani da Abba kuma dan gidan Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Ganduje ya zama dan takarar majalisar wakilan tarayya.
Abba na niyyar wakiltar mazabar Dawakin Tofa, Rimingado da Tofa.
Hadimin gwamnan jihar kan kafofin yada labaran zamani, Abubakar Aminu Ibrahim, ya sanar da cewa wanda ke neman kujerar a baya ya janyewa Abba.
Inda ya kara da cewa, sun yanke wannan shawara ne a wani zama da suka yi ada daren Alhamis.
“A daren wannan rana ta Alhamis, 26 ga watan mayu 2022, Dr. Junaidu Yakubu me neman takarar Majalisar Tarayya Mai Wakiltar Dawakin Tofa, Rimingado da Tofa ya janyewa Engr. Umar Abdullahi Ganduje Takararsa a zaben fitar da gwani na Jamiyyar APC da akayi.
“Anyi wannan zaman ne a bisa Shugabancin Sanatan Kano ta Arewa Barau I. Jibrin da Dan Majalisar Tarayya Mai Wakiltar Bichi, Hon. Abubakar Kabir Abubakar Bichi.
Taron ya samu Halartar Shugabannin Kananan Hukumomin Dawakin Tofa, Rimin Gado da Tofa, Kwamishinonin wannan yanki da Dattijan Jamiyyar APC na wannan yankin.”