Kakakin majalisar dokokin jihar Yobe, Honarabul Ahmed Mirwa Lawan, ya rasa kujerarsa a hannun Lawan Musa mai shekaru 35 dan takarar jam’iyyar PDP a mazabar Nguru II.
Jami’in hukumar zaben Yankin, Dakta Habib Muhammad ne ya bayyana sakamakon zaben, inda ya ce Musa ya samu kuri’u 6,648 yayin da ya kayar da kakakin majalissar Yobe wanda ya samu kuri’u 6,466.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zargin Sayen Kuri’a: Kwamishina A Bauchi Ya Nisanta Kansa Da Wani Faifain Bidiyo
Ya ce sauran ‘yan takarar ADC da NNPP da APM sun samu kuri’u 3,023 da 14 kowannen su.
Daily Trust ta ruwaito cewa Kakakin Majalisar Yobe ya kasance a majalisar tun 2003 lokacin da aka zabe shi a matsayin dan majalisar wakilai a karkashin jam’iyyar All Nigeria Peoples Party (ANPP).
A wani labarin kuma, Yanzu-Yanzu: Mace Ta Tika Kakakin Majalissar Filato Da Kasa
Kakakin majalisar dokokin jihar Filato, Yakubu Sanda na jam’iyyar APC ya sha kaye a yunkurinsa na komawa zauren majalisar. Kamar yadda Channels TV ta ruwaito.
Dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Mrs Happiness Matthew Akawu, ta yi nasara a zaben da aka yi a ranar Asabar din da ta gabata na neman kujerar dan majalisar wakilai ta mazabar Pengana.