Gwamna jihar Edo Mista Godwin Obaseki, ya bayyana shiga jam’iyyar PDP a ranar Juma’a da rana a sakatariyar jam’iyyar da ke Benin, babban birnin jihar, kamar yadda jam’iyyar PDP ta wallafa a shafinta na Twitter.
Obaseki ya fice daga jam’iyyar ne kwanaki kadan bayan ficewarsa daga jam’iyyar APC wacce a cikinta aka zabe si a karon farko.
A satin da ya gabata ne jam’iyyar APC ta ce Obaseki ba zai iya shiga takara a zaben fitar da gwani ba saboda a cewarta akwai bambamce-bambamce a takardun makarantarsa.
https://dimokuradiyya.com.ng/siyasa-gwamna-obaseki-ya-fice-daga-jamiyyar-apc/
Sai dai ficewar gwamna bata rasa nasaba da rikicin dake faruwa tsakaninsa da shugaban jam’iyyar Adams Oshiomole, wanda rikicin ake kallonsa a matsayin fadan yaro da mai gida.
Ranar Talata Gwamna Obaseki ya fita daga jam’iyyar APC bayan ganawarsa da Shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja yana mai cewa zai koma wata jam’iyyar domin neman takara a wa’adin mulki na biyu.
A yau juma’a ne dai gwamnan ya bayyana komawarsa jam’iyyar PDP, bayan da yayi wata ganawar sirri tsakaninsa da wasu jigajigan jam’iyyar ta PDP.
Obaseki shi ma ya bayyana komawarsa jam’iyyar PDP a kafafensa na sada zumunta.