Wani ɗan gajeran bidiyo mai ƙayatarwa na wasu sojoji mata gudu uku suna tiƙar rawa ya janyo cece-kuce manhajar TikTok.
A cikin bidiyon kyawawan sojojin sun yi kalar rawa iri daban-daban waɗanda suka yi su cikin ƙwarewa. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranakun Hutun Karamar Sallah
Sun kuma nuna suna jindaɗin rawar wanda hakan ya nuna sun ɗauke ta ne kawai a matsayin abin samun nishaɗi.
Bidiyon ya sanya mutane da dama sun tofa albarkacin bakin su, inda mutane da dama suna kalle shi sannan suka yi ɗaruruwan sharhi a kansa.
Ku kalli bidiyon a nan
Ga kaɗan daga cikin ra’ayoyin da mutane suka bayyana akan bidiyon waɗanda Dimokuradiyya ta tattaro:
@abhenahlyphstyle ya rubuta:
“Ta bayan ta fi iyawa.”
@eliasuumar ya rubuta:
“Dukkanin ku kun yi kyau.”
@Wennieb1980 ya rubuta:
“Muna godiya ƴan mata bisa ƙoƙarin ku wajen aiki da rawar ku.”
@KĀKÄ_JÜNÍØR ya rubuta:
“Boom! Ta bayan raƙashewar ta kawai ta ke yi.”
@Scorefinancials ya rubuta:
“Muna alfahari da ku ƴan mata sannan mun gode bisa sadaukarwar da kuke yi.”
“Ya Ba Maza Kunya” Bidiyon Ango Yana Sharbar Kuka a Wajen Daurin Aurensa Ya Girgiza Intanet
A wani labarin na daban kuma, wani ango ya zo da abin mamaki, bayan ya kama sharɓar kuka a wajen ɗaurin auren sa.
Wani bidiyo da ya nuna lokacin da wani ango ya kama sharɓar kuka, ya yaɗu sosai a manhajar TikTok.
A cikin bidiyon angon ya ƙasa ɓoye shaukin da angon yake ciki wanda hakan ya sanya shi zubar da hawayen farin ciki