An dake shiri’a da ake yi tsakannin Kungiyar Malaman jami’oi ta kasa wato ASUU da Ministan Kwadago Chirs Ngige ya shigar a gaban Kotu. Kamar yadda Punch ta ruwaito
An shigar da karar ne a gaban Mai’shari’a Polycarp Hamman na kotun kula da da’ar ma’aikata dake babban birnin Tarayya Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Za Mu Aike Da Atiku Gidan Ritayarsa A Dubai, Inji Shettima
Lokacin da aka fara sauraron shiri’ar Dan rajin kare hakkin Dan Adam Ebunolu Adegoruwa SAN ya bayyana Kotun cewa, shi ne mai wakilitar kungiyar Kare hakkin al’umma kuma shi ne ya shigar da karar kan wannan batu a gaban Kotun
Sai dai da yake mayar da martani Lauyan da ke kare Kungiyar ASUU Femi Falana SAN ya shaidawa Kotun cewa, kukkannin korafe-korafen aka shigar sun iso ne gareshi a ranar Litinin kuma akwai ta kaddun da yake hadawa.
Kazalika Falana ya bukaci Kotun da ta dage sauraron shiri’ar domin samun damar kammala hada dukkannin takaddun da suka kamata.
Akarshe Alkalin Kotun ya dage ci gaba da sauraron shari’ar har zuwa ranar Juma’a 16 ga watan Satumban 2022.
A WANI LABARIN KUMA: Sanata Uba Sani Ya Ƙaddamar Da Ajujuwa A Wata Cibiyar Koyar da Sana’o’i.
Dan takarar gwamnan jihar Kaduna a karkashin inuwar jam’iyyar APC Sanata Uba Sani ya kaddamar da wasu Ajujuwan karatu, a cibiyar koyar da sana’o’i a Zaria
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Sanata Uba ya tabbatar da hakan, bayan ya wallafa hotunan yadda lamarin ya kasance, a shafinsa na dandalin sada zumunta dake facebook.