Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, Dan Takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar NNPP, Buba Gakadima, Jigo a Jam’iyyar, sun yi diran mikiya a ofishin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), kamar yadda Daily Trust ta rawaito.
Mutanen biyu suna wajen ofishin INEC tare da dubban magoya bayan jam’iyyar.
KARANTA WANNAN LABARIN: INEC Ta Dage Cigaba da Tattara Sakamakon Zaben Jihar Adamawa
A wurin tattara sakamakon zaben gwamna, aka kuma bayyana alkaluma daga dukkan kananan hukumomi 44, inda jam’iyyar adawa ke kan gaba.
Sai dai kuma jami’in da ke kula da tattara sakamakon zaben kananan hukumomi jihar, ya ce yana bukatar lokaci don yin aiki kan fom din.
Hakan ya kara haifar da shakku a tsakanin wakilan jam’iyyar da magoya bayanta a zauren taron, amma jami’an zaben sun ba su tabbacin cewa komai yana a karkashin kulawa.
A wani labarin kuma, An Sake Zaber Sanwo-Olu A Matsayin Gwamnan Jihar Legas A Karo Na Biyu
Hukumar zabe mai zaman kanta ta bayyana gwamnan jihar Legas, Mista Babajide Sanwo-Olu, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan da aka gudanar a jihar a ranar Asabar, 18 ga watan Maris.
Sanwo-Olu na jam’iyyar ya lashe kananan hukumomi 19 cikin 20 na jihar a zaben.
Sanarwar ta fito ne cikin daren Litinin, 20 ga watan Maris, daga bakin jami’in zaben gwamna da na ‘yan majalisar dokoki a jihar Legas, Farfesa Adenike Oladeji.
Sanwo-Olu wanda ya samu kuri’u 762,134, ya doke abokin hamayyarsa Gbadebo Rhodes-Vivour na jam’iyyar Labour wanda ya samu kuri’u 312,329 sannan Olajide Adeniran na jam’iyyar PDP ya samu kuri’u 62,449.