Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya amince da rusa garuruwan Garki, Jabi da sauran unguwanni 28 da hukumar raya babban birnin tarayya ta yi bincike a baya kafin wannan gwamnatin, Daily Post ta rawaito.
Rushewar, a cewar FCTA, zai shafi gine-gine kusan 6,000 da aka yi wa alama a wani yunƙuri na kawar da ƙayatattun gidaje da gine-ginen da akayi su ba bisa ƙa’ida ba.
KARANTA WANNAN: Tinubu Ya Taya Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III Murnar Cika Shekaru 67
Hukumar ta FCTA ta ce rusau din zai shafi yankuna 30 a fadin babban birnin tarayya Abuja.
A ranar Litinin bayan rantsar da shi a matsayin Minista, Wike, wanda shi ne tsohon gwamnan jihar Ribas, ya sha alwashin dawo da babban tsarin na babban birnin tarayya Abuja, inda ya ce za a ruguza duk wasu gine-ginen da ba su dace ba, kuma gwamnatinsa a shirye ta ke ta kawo karshen cece-kucen filaye.
Ya ce ya zagaya da daddare cikin babban birnin tarayya Abuja domin ya ga al’amura da kansa, ya kuma koka da yadda tsarin mulkin yankin ya karkata da wasu gine-ginen da ba a saba gani ba a Abuja, yana mai cewa za a rusa su.
“Akalla haramtattun gine-gine 6,000 a babban birnin tarayya Abuja gwamnatin tarayya zata ruguje su a yankuna 30.
Wike ya ce: “Za mu mayar da ƙasarmu mu ba wa waɗanda suke son haɓakawa, kuma dole ne ku sanya hannu kan cewa dole ne ku ci gaba a lokaci guda.”
Sai dai Daraktan Sashen Kula da Cigaban Ƙasa na FCTA, Muktar Galadima ya ce za a gudanar da wani sabon bincike.
“Za mu sami lokaci don komawa mu gudanar da wani sabon bincike, lura da cewa binciken na karshe da aka yi shi ne a watan Fabrairun shekarar 2022.
Wuraren da aka yiwa alamar rugujewa bisa ga bayanin da hukumar FCTA ta tabbatar sune:
1. Apo Mechanic Village
2. Byanzhin.
3. Dawaki
4. Dai Dai.
5. Durumi.
6. Dutse.
7. Garki.
8. Garki Village.
9. Gishiri.
10. Gwagwalada.
11. Idu.
12. Jabi.
13. Kauyen Kado.
14. Karmo.
15. Karshi.
16. Karu.
17. Katampe.
18. Kauyen Ketti.
19. Kpaduma.
20. Kabusa.
21. Kauyen Kpana.
22. Kubwa.
23. Lokogoma.
24. Lugbe.
25. Mabushi.
26. Mpape.
27. Nyanya.
28. Piya Kasa.
29. Jikwoyi
30. Galadima
A wani labarin kuma, Ambaliyar Ruwa: NEMA ta Raba Kayan Agaji Ga Sama Da Mutane 9k da Abin Ya Shafa
Hukumar NEMA ta bawa mutanen da basu gaza 9000 ba da ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Yobe tallafi
An kaddamar da rabon kayayyakin a cibiyar taron dake gidan gwamnatin jihar.
An yi kira ga duk wadanda suka amfana da su yaba tare da mayar da hankali wajen yin amfani da kayayyakin yadda ya kamata tare da kaucewa sake sayar da su
Yanzu haka dai mutanen da basu gaza 9000 ba da ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Yobe ne za su ci gajiyar shiga tsakani don dakile mummunan bala’in ta hanyar agajin gaggawa na rayuwa na musamman na kasa (SNELEI) wanda Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta aiwatar.
Gwamnan jihar Mai Mala Buni ne ya kaddamar da rabon kayayyakin a cibiyar taron dake gidan gwamnati a Damaturu.