Aƙalla mutum uku sun rasa ransu yayin da wasu mutum shida suka jikkata bayan wasu motoci biyu sun yi taho mu gama a kan titin hanyar Abuja-Kaduna.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, wani shaidar ganau ba jiyau ba, Saidu Ibrahim, ya bayyana cewa lamarin ya auku ne a ƙauyen Mararaban Ida A safiyar ranar Asabar.
KU KARANTA KUMA: Yan Sanda Sun Tabbatar Da Sace Yara A Zamfara, Bayan Masu Garkuwar Sun Tafi
Ya bayyana cewa motocin da aka yi haɗarin da su akwai wata mota ƙirar Toyota Highlander mai rajistar KWL 198 KA da Volkswagen golf mai rajistar MKA 89 ZY.
Ibrahim yace direban Highlander ɗin wacce ke tahowa daga ɓangaren Kaduna cikin sauri cikin ganganci ya wuce wata mota inda ya haɗe da motar Golf ɗin wacce take tahowa daga ɓangaren Abuja.
“Direban golf ɗin yana tahowa ne daga ɓangaren Abuja motar sa cike da lemu da sauran kayan marmari inda ya nufi ƙauyen Gidan Abe, lokacin da motar Highlander jeep ɗin ta taho da gudu bayan an sauya hannu ta haɗe da golf din.”
Wakilin majiyar mu da ya ziyarci wajen jim kaɗan bayan aukuwar lamarin, yayi arba da gawarwaki biyu daga motar golf ɗin yashe a bakin titi.
Ya kuma ga wasu jami’an FRSC suna ƙoƙarin ciro direban wanda ya maƙale a cikin motar.
Mutum bakwai ɗin da suka samu raunika an kai su babban asibitin Sabon Wuse.
Wani jami’in FRSC wanda da shi aka yi aikin ceton, yace waɗanda haɗarin ya ritsa da su, gawarwaki ukun an miƙa su ga ƴan’uwan su bayan sun shaida su a wajen.