By Abbas Yakubu Yaura
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Juma’a, ya koma Abuja bayan ya halarci toron shirin kare muhalli na Majalisar Dinkin Duniya a Nairobin kasar Kenya.
Wannan dai ya saba wa shirin da ke kunshe cikin wata sanarwar manema labarai da fadar shugaban kasar ta fitar a baya, inda ta bayyana cewa shugaban zai wuce birnin Landan domin duba lafiyarsa bayan kammala shirin na kasar Kenya.
Yayin da yake kasar Kenya, shugaban ya halarci wani zama na musamman don tunawa da cika shekaru 50 na Majalisar Dinkin Duniya.
Buhari ya ce: “A yayin da muke murnar cika shekaru 50 da kafuwar UNEP, muna yaba wa kokarin UNEP tare da karfafa daukar matakai don shawo kan sauyin yanayi, rabe-raben halittu, karuwar gurbatar yanayi da sharar gida kasancewar manyan matsaloli uku da ke barazana ga duniyarmu.
Shugaban ya kuma gana da Mista Ibrahim Thiaw, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya don yaki da hamada (UNCCD) a Nairobi.
A yayin ganawar, Buhari ya ba da umarnin hadin gwiwa tsakanin ma’aikatun muhalli, albarkatun ruwa, noma da raya karkara da makamashi domin yaki da kwararowar hamada.