Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana dalilan da yasa ba za a iya biyan bashin Naira biliyan 1.6 da hukumar shirya jarrabawar Afirka ta Yamma (WAEC) ke binsu ba nan take.
A ranar Litinin din da ta gabata ne hukumar WAEC ta sanar da cewa gwamnatin jihohi takwas na Najeriya
Na da bashin da basu biya ba,daga kudaden rijistar dalibai da suka amince da daukar nauyin gudanar da jarabawar na wasu shekaru.
Shugaban ofishin WAEC na Najeriya, Patrick Areghan, a lokacin da yake jawabi ga taron sanar da fitar da sakamakon jarrabawar 2023 West African Senior School Certificate (WASSCE) na ‘yan makaranta.
Ya bayyana cewa wadanda suka fito daga jihohi takwas da hukumar jarabawar ke bin kudi ba za su sami damar samun sakamakonsu har sai jihohin sun biya.
Ko da yake Mista Areghan bai bayyana sunayen jihohin da ake bin bashin ba, amma an lura cewa “jihohin Zamfara da Neja ne suka fi cin bashi.
A wata hira da PREMIUM TIMES ta wayar tarho a ranar Talata, babban mai taimaka wa Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara kan harkokin yada labarai da hulda da jama’a, Mustapha Kaura, ya tabbatar da cewa WAEC na bin Jahar bashin kimanin Naira biliyan 1.6
KARANTA NANKu Godewa Allah Wata Kasar Ta Fiku Tsadar Rayuwa-CBN Ga Yan Najeriya
Mista Kaura ya ce basussukan sun taru a tsawon lokaci daga tsohuwar gwamnatin tsohon Gwamna Bello Matawalle da ta tsohon gwamnan jihar, Abdulazeez Yari.
Ya ce WAEC ta ci gaba da baiwa wasu jahohin da suka biya kuma amintattu wadanda ke biyan kudin rajistar dalibansu.
Abin takaici jaha Kamar Zamfara ace bata biya kudin Jarabawar WAEC ba domin daliban jahar su samu damar samun sakamakon su cikin lokaci.
Mista Kaura ya ce gwamnati ta kuduri aniyar biyan bashin gaba daya ko kuma a dunkule amma gwamna na jiran ya samu amincewa da zarar an kafa majalisar kwamishinoninsa.
A WANI LABARIN KUMAGwamnatin Najeriya Ta Baiwa Sanatoci Kudin Rage Radadin Cire Tallafin Man Fetur-Akpabio
Mai magana da yawun gwamnan ya ce “N1.6bn sun wuce amincewar gwamnan ba tare da wani bangare ba. Dole ne ya nemi amincewar majalisar zartarwa ta jiha kamin fitar dasu.