Kotun ƙoli ta tabbatar da nasarar gwamna Yahaya Bello na jam’iyyar APC a zaɓen gwamnan jihar Kogi na ranar 16 ga watan Nuwamban 2019.
A safiyar Litinin alƙalan kotun guda bakwai suka yi watsi da ɗaukaka ƙarar da ɗan takarar Jam’iyyar PDP a zaɓen, Musa Idris ya yi bisa zargin cewa Yahaya Bello bai ci zaɓen ba.
Alƙalin da ta jagoranci zaman, Uwani Abba-Aji, ta ce masu ɗaukaka ƙarar sun kasa tabbatar da zarge-zargen da suka ɗaukaka ƙarar a kai.
https://dimokuradiyya.com.ng/zaben-gwamna-a-kogi-zan-garzayan-kotu-dan-takarar-pdp/
Musa Idris na zargin an yi rikicin siyasa a zaɓen, na’urar tantance masu zaɓe ba su yi aiki yadda ya kamata ba, sannan ƙuri’un da aka kaɗa sun fi yawan mutanen da aka tantance a zaɓen.
Tun da farko kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Kogi wadda ta yi zamanta a Abuja ta yi watsi da zargin ɗan takarar. Daga baya a watan Agusta kotun ɗaukaka ara ta tabbatar da hukuncin.
Ana dakon hukuncin da alkalan kotun za su yanken game da karar da ‘yar takarar Jam’iyyar SPD a zaben, Natasha Akpoti, ta daukaka, na kalubalantar sakamakon zaben.