Wata budurwa ƴar Najeriya ta sha alwashin ba zata ƙara fara cewa tana son wani namiji ba, bayan da tayi a karon farko ba taji da daɗi ba.
“Da in ƙara cewa ina son wani namijin gwara na tafi a karkace,” budurwar mai amfani da sunan @NanaFirdausiii, ta rubuta a shafin ta na Twitter, tare da alamun kuka yayin da ta sanya hirar ta da wani saurayi mai suna Bash-Aar.
KU KARANTA KUMA: Daga ƙarshe Tinubu ya bayyana gaskiya dangane da batun ƙara auren sa.
Jaridar Legit.ng ta rahoto cewa daga cikin hirar ta su, budurwar ta tambayi saurayin ko baya da budurwa, inda ya bata amsar da ba tayi mata daɗi ba.
Hakan bai sanya ta karaya ba, inda ta ƙara gwada neman sa’ar ta, take ce masa ta daɗe tana bibiyar sa kuma yana birgeta.
Ta ƙara da cewa ita kyakkyawa ce sannan ta roƙi Bash-Aar da ya bata dama. Saurayin ya haƙiƙance cewa yana da wacce yake so amma duk da haka budurwar ta nace.
Ta kuma cigaba da gaya masa tana da kuɗi amma yayi mata wani martani mai zafi.
Mutane da dama sun tofa albarkacin bakin su kan yadda saurayin ya ƙi karɓar tayin soyayyar da budurwar tayi masa ba.
Ga kaɗan daga cikin waɗanda Dimokuradiyya ta tattaro:
@aeykaey_bamalli ya rubuta:
“Ni yakamata ki turawa wannan saƙon amma aa wanda yake da budurwa kika je kina nema.”
@Rufai_NBA ya rubuta:
“Nayi tunanin zaki fahimci halin da yake ciki, amma baki fahimta ba. Ya riƙe wa budurwar sa amana sannan baki san a wane mataki suke ba.”
@oluwagallant01 ya rubuta:
“Kada ki karaya ƴar’uwata. Ki cigaba da ƙoƙartawa. Ta iya yiwuwa baya son yayi arha ne a wajenki idan ya yarda nan take.”
@Aloyesamuel ya rubuta:
“Maganar gaskiya, ban ga wani laifi ba kan abinda yace. Gaskiyar sa ya faɗa ko tantama babu. Kawai dai ya tsaurara ne wajen kin karɓar ki. Ban ga wani rashin mutuntawa ba a amsoshin da ya bayar.”
“Har Yanzu Da Ƙwari Na” Cewar Magidanci Mai Ƴaƴa 126 Da Ya Ƙaro Aure
A wani labarin na daban kuma, wani magidanci mai ƴaƴa ɗari da ashirin da shida ya sake sabon aure, yace har yanzu da sauran ƙwarin sa.
Wani magidanci mai ƴaƴa ɗari da ashirin da shida yayi aure a karo na goma sha ɗaya, duk da ya tsufa.