Wani magidanci mai ƴaƴa ɗari da ashirin da shida yayi aure a karo na goma sha ɗaya, duk da ya tsufa.
Magidancin mai suna Ali Al Balawi, ɗan ƙasar Saudiyya ne kuma yana da shekara tamanin da uku a duniya.
Yayi murnar auren sa ƙaro na sha ɗaya tare da haɗa wani gagarumin shagalin biki wanda ƴan’uwa da abokan arziƙi suka halarta. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
KU KARANTA KUMA: Surikata bata bari mu raya sunnah nida mijina -Matar aure ta koka
Da zuwan wannan sabuwar amaryar tasa, Ali yanzu yana da mata huɗu a tare da shi duk kuwa da sau goma sha ɗaya yayi aure.
Ali yana da ƴaƴa maza goma sha takwas, ƴaƴa mata ashirin da jikoki maza da mata tamanin da takwas.
Ali ya kare tara iyalai da yawa da yayi inda yake cewa yana da halin da zai kula da su duk da cewa ana masa kallon ya tsufa.
Ali yace a shekarun sa 83, har yanzu yana da hankali, ƙarfi da halin da zsi oya kulaws da iyalan da yake da su.
A kalamansa:
“Babu wani abinda zai hanani ƙara aure. Ina da arziƙi, hankali da ƙarfin da zan iya riƙe mata hudu.”
Ya bayyana cewa baya fuskantar wata matsala a gidan sa saboda yana yiwa matan sa adalci. Ali ya shawarci mazaje da su ƙara aure a irin shekarun sa idan har suna da cikakkiyar lafiya.
An dai yi shagalin bikin auren Ali karo na sha ɗaya ne a Tabuk, yankin Arewa maso Yamma na ƙasar Saudiyya.
Daga Ƙarshe Tinubu Ya Bayyana Gaskiya Dangane Da Batun Ƙara Auren Sa
A wani labarin na daban kuma, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC ya bayyana gaskiya dangane da batun yiwa matarsa kishiya.
Ɗan takarar kujerar shugaban ƙasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, yayi watsi da raɗe-raɗen da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta cewa yana shirin ƙara aure.
Tsohon gwamnan na jihar Legas wanda ya bayyana rahotannin a matsayin “labaran ƙarya” yace yana jindaɗin auren sa da matarsa ɗaya tilo Sanata Oluremi Tinubu