Yan ta’addan da suka kai hari kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun sake sakin wasu fasinjoji 5 da suka yi garkuwa da su a yau Talata.
Mutane 5 da abin ya shafa su ne Farfesa Mustapha Umar Imam, Akibu Lawal; Abubakar Ahmed Rufa’i Mukthar Shu’aibu da Sidi Aminu Sharif.
Yayin da yake tabbatar da sakin su ga manema labarai a Kaduna, jagoran sasantawa kuma mai ba wa Sheikh Ahmad Gumi shawara kan harkokin yada labarai; Malam Tukur Mamu ya ce kamata ya yi gwamnati ta gaggauta yin shawarwari domin ganin an sako sauran wadanda aka yi garkuwa da su domin suna cikin hadari.
Ya kuma yi kakkausar suka masu cewa tattaunawa bata da amfani, inda hakan akwai muhimmanci a ciki sosai wato tattaunawa da ‘yan ta’adda, yana mai jaddada bukatar hakan.
“A yanayin da rundunar soji ba za ta iya aiki ba, tabbas tattaunawa za ta yi aiki,” in ji shi.
Dukkanin wadanda aka sako kwanan nan sun mika godiyarsu ga Allah tare da godewa Tukur Mamu bisa rawar da ya taka yayin tattaunawa da wadanda suka yi garkuwa da su.