…Hukumar zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana Rt. Honarabul Francis Nwifuru na jam’iyyar (APC) a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna na 2023 a
Hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa Rt. Honarabul Francis Nwifuru na jam’iyyar (APC) ne ya lashe zaben gwamnan jihar Ebonyi na 2023.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Nwifuru wanda shine kakakin majalisar dokokin jihar ya samu jimillar kuri’u 199,131.
Sai kuma dan takarar jam’iyyar (PDP), Mista Ifeanyichukwuma Odii, wanda ya samu kuri’u 80,191.
KU KARANTA KUMA Jami’an Tsaro Sun Bindige Wani Dan IPOB A Ebonyi
Dan takarar jam’iyyar (APGA), Farfesa Bernard Odo, ya zo na uku da kuri’u 52,189.
“Ni Farfesa Charles Igwe a nan na bayyana cewa Nwifuru Francis na gamsu da yadda aka gudanar da zabe kuma na bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben,” in ji jami’in zabe na INEC.
Farfesa Igwe ya sanar da sakamakon da misalin karfe 2:30 na rana. Hakan ya zo ne sa’o’i 48 bayan wata cece-ku-ce a cibiyar tattara sakamakon zabe ta INEC da ke Abakiliki.
Jaridar Daily trust ta tattaro cewa sakamakon daga kananan hukumomin Ikwo, Ezza North da Ishielu ya haifar da cece-kuce a cibiyar tattara sakamakon.
Takaddamar dai ta kasance tsakanin wakilin jam’iyyar PDP na jihar, Barista Mudi Erhinedu da na APC, Honarabul Austin Umahi.
Sai dai wakilin jam’iyyar APGA na jihar, Sanata Emmanuel Onwe, ya ki sanya hannu kan sakamakon yayin da na PDP ya sanya.
A Wani Labarin Kuma Gwamna Umahi Ya Kori Wasu Mataimakansa Sa’o’i 48 Bayan Kammala Zabe
Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya kori mambobin wasu hukumomi mallakar jihar, da kwamitoci da ko’odinetocin cibiyoyi 64 na jihar.
An umurci mutanen da abin ya shafa da su mika dukkan kadarorin gwamnati da suka hada da motocinsu na hukuma da ke hannunsu a yau ko kuma kafin rufe ofishi a ranar Litinin din nan.