…Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya kori mambobin wasu hukumomin jihar, da kwamitoci da ko’odinetocin cibiyoyi 64 na jihar
Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya kori mambobin wasu hukumomi mallakar jihar, da kwamitoci da ko’odinetocin cibiyoyi 64 na jihar.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa An umurci mutanen da abin ya shafa da su mika dukkan kadarorin gwamnati da suka hada da motocinsu na hukuma da ke hannunsu a yau ko kuma kafin rufe ofishi a ranar Litinin din nan.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da ma’aikatan gwamnati da aka fitar ranar Litinin kuma sakataren gwamnatin jihar Ebonyi, Dr.Ugbala Kenneth ya sanya wa hannu.
KARANTA HAKANAN Umahi Ya Bukaci Kwankwaso Da Sauren Yan Takara Da Su ceto Nigeria
“Gwamnan jihar Ebonyi, David Umahi, ya amince da rusa kwamitoci, mambobi, da masu kula da cibiyoyi na ci gaba ba tare da bata lokaci ba, banda majalisar gudanarwar jami’ar jihar Ebonyi.
“Saboda abubuwan da suka gabata, ko’odinetocin cibiyoyi na ci gaba za su mika dukkan kadarorin gwamnati da ke hannunsu ciki har da motocinsu na hukuma ga ofishin sakataren gwamnatin jihar da kwamishina mai kula da harkokin gwamnati, a ko kuma kafin rufe aiki a ranar Talata 21 ga watan watan Maris 2023.
“Hakazalika, hukumomi da kwamitocin su mika kadarorin gwamnati da ke hannunsu ga ma’aikatun da ke sama da su a ko kuma kafin rufe aiki a ranar Talata, 21 ga watan Maris, 2023,” in ji sanarwar a wani bangare.
Dalilin da ya sa gwamnan ya dauki matakin ya biyo bayan sa’o’i 48 da gudanar da zaben gwamna da na ‘yan majalisar dokokin jihar baya cikin sanarwar.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Amma wata majiya mai tushe ta danganta hakan da rashin aiki da almubazzaranci da kudade da aka saki a baya ga masu gudanarwar cibiyoyin 64 na raya kasa na zaben ranar 18 ga watan Maris.
Haka kuma, daya daga cikin masu gabatar da kara da bai so a ambaci sunansa ba, ya shaida wa wakilinmu cewa wasu daga cikinsu ba su iya samun kudi kafin zaben ranar Asabar.
Har yanzu ana ci gaba da tattara sakamakon zaben gwamna a jihar.
A Wani Labarin Kuma INEC Ta Bayyana Wanda Ya Lashe Zaben Gwamna A Jihar Filato
An bayyana dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Filato, Caleb Mutfwang a matsayin wanda ya lashe zaben da ya gudana ranar Asabar.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC ta bayyana hakan a ranar Litinin.