Majalisar wakilai ta Kasa ta caccaki jirgin Nijeriya Air wanda aka kaddamar a lokacin gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Majalisar ta bayyana kaddamar da jirgin na Najeriya a matsayin damfara.
Shugaban kwamitin majalisar kan harkokin sufurun jiragen sama, Nnolim Nnaji ya bayyana kaddamar da kamfanin na Nigeria Air a matsayin yaudara bayan da manyan masu ruwa da tsaki a yarjajeniyar da aka yi tsakanin gwamnatin tarayya da kamfanin jiragen saman na Habasha suka musanta labarin kaddamar da jirgin.
KARANTA WANNAN Jirgin SamanNigerian Air Zai Fara Aikin Ranar Litinin – Sirika
Ma’aikatar sufurin jiragen sama ta yi ikirarin cwa an kaddamar da jirgin na Nigeria Air ne kawai amma ba gaske bane, wanda kwamitin ya yi watsi da shi a matsayin yunkurin karkatar da hankalin ‘yan majalisar.
Mambobin kwamitin sun kadu a lokacin da NAMA ta bayhana cewa jirgin mai dauke da kalar Nigeria na cikin wani jirgi da ak yi hayarsa zuwa Najeriya.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa Sauran masu ruwa da tsaki da suka tabbatar da bayanin sun lura da cewa jirgin da aka yi hayar za a iya yi masa kowane fentin launi da kowane rubutu.
A Wani Labarin Kuma Kwankwaso Ya Yi Magana Akan Tsohon Sarkin Kano
Tsohon gwamnan jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso ya mika sakon ta’aziyya da godiyarsa ga marigayi Sarkin Kano Ado Bayero ya wanda ya rasu
a watan Yunin 2014.
Sarkin wand guda ne cikin shugbannin addinin musulinci da ake girmamawa, kuma mai sukar mayakan Boko Haram.