Tsohon gwamnan jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso ya mika sakon ta’aziyya da godiyarsa ga marigayi Sarkin Kano Ado Bayero ya wanda ya rasu a watan Yuni na shekarar 2014.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa, Sarkin wanda guda ne cikin shugbannin addinin musulinci da ake girmamawa, kuma mai sukar mayakan Boko Haram.
KARANTA WANNAN Abba Gida Gida Zai Binciki Batun Tsige Sarki Sunusi – Kwankwaso
Ya rasu yana da shekaru 83 a watan Yunin 2014 bayn ya yi fama da rashin lafiya jim kadan bayan ya dawo daga Landan, inda yake jinya.
Da yake tunawa da marigayi Sarkin bayan shekaru 9 da rasuwarsa dan takarar shugaban Kasa a jam’iyyar NNPP a zaben ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, Kwankwaso a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce marigayin mutum ne mai martaba a idanun daukacin al’ummar jihar Kano.
Ya ce “A wannan rana, muna tunawa da mahaifinmu marigayi majibincin lamuran al’umma da baya gajiyawa ga daukacin mutanen Kano”
“Marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, wanda ya rasu shwkaru tara da suka gabata ya bar mana gadon da muke mutuntawa kodayaushe, Allah ya yi Sarki rahama. Allah ya taimaki Kano da Kanawa, amin” inji Kwankwaso.
Kafin Alhaji Ado Bayero ya hau karagar mulki ya yi aiki a matsayin ma’aikatcin banki, Dan Sanda, jami’in diflomasiyya, ya kuma kasance hamshakin dan kasuwa.
Jaridar PUNCH ta rawaito cewa Duk da cewa Sarkin Musulmi shi ne babban shugaban Musulmin Nigeria, amma mutane da yawa suna kallon marigay Sarkin Kano Alhajj Ado Bayero a matsayin wanda ya fi kowa daraja da kuma tasiri a Kasar nan.
A Wani Labarin Kuma Zamba: EFCC Ta Gurfanar Da Wasu Ma’aikatan Banki Guda Biyu
Hukumar da ke yiki da masu yi wa tattalin arzikin Kasa zagon Kasa EFCC a ranar Talatar nan ta gurfanar da wasu ma’aikatan banki guda biyu Freeman Jacob da Umar Abdullahi a gaban mai shari’a Akgah Amobeda na babbar kotun tarayya da ke Kano.
An gurfanar da matasan biyu bisa tuhumarsu da laifuka uku da suka hada da hada baki da satar kudi.