- An kama wani ɗan Najeriya bayan ya yi wa matarsa, mahaifiyarta da ƙanwar matarsa ciki
- Wani ɗan Najeriya ya yi wa ‘yan kasar Afirka ta Kudu ciki bayan da ya yi wa matarsa ciki da mahaifiyarta da kuma ‘yar uwarta ciki waɗanda yake soyayya dasu a asirce.
- An kama mutumin ne bayan da matarsa ta bankaɗo sirrin kuma ta kai rahoto ga hukumomi a Burtaniya, inda suke da zama.
Mutumin ya kasance yana soyayya da surukarsa da kuma kanwar matarsa a asirce.
A cikin hotuna da ke zagayawa a shafukan sada zumunta, ɗan Najeriyar ya bayyana an daure shi da hannu sannan kuma hukumar ‘yan sanda ta United Kindom ta kai shi ofishin ‘yan sanda.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ina Alfahari Da Kasancewata Namiji Amma Mai Siffar Mata Har Da Mama.
Har yanzu dai ba su fitar da wata sanarwa da ke karin bayani kan kamun ba.
Masu amfani da shafukan sada zumunta sun cika da mamaki da ban dariya kan yadda ɗan Najeriya da ya yiwa matarsa ciki, mahaifiyarta da kuma ‘yar uwar matarsa ciki a lokaci guda.
Duba ra’ayoyinsu a kasa.
Muya Mbango ya ce: “Mene ne laifin? Matan fq manya ne ba yara ba sun yarda su yi jima’i ba tare da kariya ba, kuma duk sun sami juna biyu… menene batun laifi a nan?”
Youth_Nation ya ce: “Bari mu bincika a Guinness idan mutumin bai karya wani tarihi irin wannan ba.”
Sue Diamond ya ce: “Eeehhi Yezu Kristo, amma ina ganin ya kamata a kama matan su ma – (mahaifiyar matar da ‘yar uwar matar) sai dai idan ya yi musu fyaɗe ne.”
Eagle Tropojan: “A koyaushe na ce, kada ku kwana tare cikin duhu da mata daban-daban. Babu wanda zai san wadda yake mu’amula da ita a duhu. Alhamdu lillahi, su kam dai sun samu lafiya, ba ciki ba.”
James Lynch ya ce: “Kada ‘yan sanda su tarwatsa wannan dangin dake cikin farin ciki saboda ban ga laifi a nan ba. Lallai ɗan Najeriya ya zura kwallaye uku rigis a raga”
Mbulazi Mtungwa ya ce: “Na zargi matar da gaya wa ‘yar uwarta da mahaifiyarta irin daɗin da take sharɓa wajen mijinta, hakan yasa suma suka laɓaɓa don samun rabon su.”
Bike na Xolile ta ce: “To yayanmu na wata ƙasar a kula da inda zaku dinga ajiye bukatun ku”
Peach ta ce: yiwa mata ciki a Ingila yanzu laifi ne ke nan.”