• Anyi harbe-harbe, bayan Shugaban Majalisar Imo ya dakatar da Shugaban Marassa Rinjaye,
• ya Kuma dakatarda wasu yan Majalisa guda 5.
• Lamarin ya farune yayin wani zaman gaggawa da majalissar ta gudanar a yau.
Ana cigaba da nuna bakin ciki da jimami, a Majalisar Dokokin Jahar Imo dake Owerri, Babban Birnin Jahar, biyo bayan Shugaban Majalisar Paul Emezim ya dakatar da Shugaban Marassa Rinjaye Anyadike Nwosu, da wasu Yan Majalisa guda 5 a ranar Alhamis.
A zaman Majalisar na gaggawa Wanda gudana cikin tsaro, Shugaban Majalisar ya dakatar da Yan Majalisar har sai baba ta gani akan abinda ya Kira ” rashin da’a ga Majalisar”
Baya ga cewa Shugaban Marassa Rinjaye Wanda Dan Jami’iyyar PDP ne, sauran Wanda Shugaban Majalisar ya dakatar, akwai Wanda ya sauka daga Mukamin Shugaban Masu Rinjaye Uche Ogbuadu Mai wakiltar Ikeduru daga Jami’iyyar APC, da Onyemaechi Njoku daga Jami’iyyar APC Mai wakiltar Ihitte-Uboma, sai Kennedy Ibeh daga Jami’iyyar APC Mai wakiltar Obowo, da Kuma Philip Ejiogu daga Jami’iyyar PDP Mai wakiltar Owerri ta kudu, gami da Dominic Ezerioha Mai wakiltar Oru ta Yamma daga Jami’iyyar APC.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hukumar kula da harkokin Yan sanda ta ki amincewar da Karin girman da akayiwa Ibrahim Magu
Emezim ya Kuma rusa dukkanin kwamitoci na Majalisar, tare da cire Shugaban Masu horaswa na Majalisar Authur Egwumim wanda Dan Jami’iyyar APC ne mai wakiltar Ideoto ta Arewa, tare da musanya shi da Obinna Okwara Mai wakiltar Nkwerre daga Jami’iyyar APC.
Wannan al’amari ya haddasa bakin ciki da jimami, inda Jami’an tsaron Shugaban Majalisar suka harba bindiga a sama, domin samar da hanyar da Shugaban Majalisar ya fita daga Majalisar, a sa’ilinda aketa Zanga-zanga nuna rashin amincewa.
Daya daga cikin Yan Majalisar da aka kora Ibeh yace ” mun samu sako daga akawun Majalisar cewa akwai zaman gaggawa a yau Alhamis, tunda a jiya Laraba an daga zaman har sai 14 ga watan Juli.
“Munzo Majalisar tun karfe 10 amma bamu ga Shugaban Majalisar ba, mukai ta jira har saida ya karaso ya Shiga zauren Majalisar ya sanya hannu a rajista. Shugaban Majalisar ba tare da la’akari da dokar Majalisar ba, ya rusa dukkanin kwamitoci da kuma Shugaban masu horaswa tare da sanar da Obinna a matsayin Wanda ya canje shi”.
“Shugaban Majalisar yace an dauki matakin ne a lokacin zaman Majalisar, alhali babu wani cikakken zama da akayi. Dan Majalisa Onyemaechi Njoku yace ya tashi tsaye a dokar tashi da ake badawa a Majalisar, amma Shugaban Majalisar yayi mashi tsawa. Nima na tashi zanyi magana yaki bani dama.
“Yaki la’akari da dokar Majalisar inda yayi amfani da tashi. Sauran Yan Majalisar sun nuna damuwar su, amma yaki duba hakan. A karshe, yace ya dakatar da 6 daga cikin mu, sakamakon munyi abinda ba dabi’ar Majalisa ba”
A lokacin da akayi mashi tambaya akan minene matakin dazai dauka, “Ibeh yace idan akayi la’akari da siyasa ni Mamba ne a Jami’iyyar APC, Kuma Gwamna shine Shugaban Jami’iyyar.
“Zan jira inyi magana da Gwamna, domin ingaya mashi bangaren nawa Labarin. Amma a maganar Majalisa wannan bani da dama. Nasha wahala siyasa a Majalisar, to na dauki wannan a matsayin wahalar Majalisa.
Daya daga cikin Mai Taimakawa Shugaban Majalisar Chukeudi Osuji ya gayawa Yan Jarida cewa dakatarwar ta dindindin ce.
Wani Kuma ya gayawa Wakilin Jaridar Punch cewa, dakatar da Yan Majalisar guda shida baya rasa nasaba da akan yadda Yan Majalisar suka damu akan yadda ake kashe kudi wajen tafiyar da Jahar.
Comments 1