• Baban koto dake Abuja ta dakatar da yunkurin Yan majalissar dokokin jihar Zamfara na tsige Mataimakin Gwamnan jihar.
• Mahadi Gusau sai ya ki amincewar da tsarin da Gwamnan jihar ya dauka na sauya sheka daga Jam’iyar Adawa ta PDP zuwa Jam’iyar Mai Mulki ta APC.
• Mai Shari’a Obiora Egwuatu na Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ne ya umarci majalissar dokokin jihar da kar ta kuskura ta tsige Mahadi Gusau daga mukamin shi.
Babbar Kotun Tarayya dake Abuja, ta tsaida yunkurin da Majalisar Dokokin Jahar Zamfara keyi, na cire Mataimakin Gwamna Mahdi Gusau.
Tuni dai rahotanni suke ta yawo cewa Yan Majalisar, na yunkurin cire Mataimakin Gwamnan Mahdi Gusau, Wanda ya’ki komawa Jami’iyyar APC, a lokacin guguwar fita daga Jami’iyyar PDP a Jahar.
Gwamna Bello Matawalle da Yan Majalisar Tarayya dana Jaha, sun canja Sheka zuwa Jami’iyyar APC a watan daya gabata.
Kwanaki Kadan bayan sun canja Sheka, Mahdi Gusau yayi gangami da yan Mambobin Jami’iyyar shi a Jahar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ana shirye shiryen Sallah: Mota ta yi hatsari, mutane 28 sun mutu
Wannan ya sanya Yan Majalisar Jahar sunyi karar shi, akan dai-dai lokacin da yayi gangamin, bayan ana cigaba da Kashe Jama’a a Jahar.
Amma a hukuncin daya yanke a ranar Litinin, Mai Shari’a Obiora Egwuatu na Babbar Kotun Tarayya dake Abuja, ya bayar da umarnin kada su kuskura su cire Gusau.