An saki tsohon Darakta-Janar na kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na Jam’iyyar Labour Party (LP), Doyin Okupe. Kamar yadda The Nation Ta ruwaito.
Jami’an tsaro na farin kaya (DSS) sun kama Okupe a safiyar ranar Alhamis a filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dandazon Jama’ar Da Suka Fito A Onitsha Ya Nuna Cewa, Peter Obi Ne Zai Lashe Zabe — COSEYL
Kakakin hukumar ta DSS, Dr Peter Afunanya, wanda ya tabbatar da kama Okupe, ya ce an kama Okupe ne a bisa laifukan da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ke tuhumar, tare da mika musu shi.
Sai dai Okupe a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter mintuna kadan da suka gabata ya tabbatar da sakin sa daga hannun hukumar ta EFCC.
A wani labarin kuma, WHO Ta Ankarar Kan Amfani Da Wani Maganin Tari
Hukumar lafiya ta duniya ta yi gargadi game da amfani da maganin tari na Indiya guda biyu ga yara da ake kan karkara a Uzbekistan. Kamar yadda BBC ta ruwaito.
WHO ta ce magungunan, wanda Marion Biotech ya kera, “na da karancin inganci” kuma kamfanin ya gaza bayar da tabbacin kare lafiyarsu.
Sanarwar ta zo ne makonni bayan da Uzbekistan ta yi zargin cewa yara 18 ne suka mutu bayan sun sha maganin da kamfanin ya yi amma har yanzu kamfanin bai ce uffan ba game da faɗakarwar.