Jami’in hulda da jama’a na babbar jam’iyyar adawa ta PDP reshen jihar Gombe, Murtala Usman Dukku ya fice daga jam’iyyar ya koma jam’iyyar NNPP.
Ya koma jam’iyyar NNPP ne bayan ficewar sa daga jam’iyyar PDP a ranar Laraba kamar yadda wata wasika da ya aike wa jam’iyyar a unguwar sa.
KARANTA WANNAN LABARIN: WHO Ta Ankarar Kan Amfani Da Wani Maganin Tari
Idan dai za a iya tunawa jam’iyyar PDP ta dakatar da Murtala Usman ne ta wata wasika mai dauke da kwanan watan 22 ga watan Disambar shekarar 2022, mai dauke da sa hannun sakataren jam’iyyar PDP na jihar, Adamu Abubakar, inda ta zarge shi da yi wa jam’iyyar aiki.
Sai dai ya fice daga jam’iyyar sa’o’i biyu da dakatar da shi ta hanyar wata wasika da ya aikewa shugabannin jam’iyyar.
Murtala Usman ya fice daga PDP zuwa NNPP a ranar Laraba, 11 ga watan Janairu, 2023.
A baya-bayan nan dai an yi ta samun rikidewar sauya sheka daga jam’iyyar APC mai mulki da kuma PDP, inda ake ci gaba da fafatawa a jam’iyyun biyu.
Shugaban shiyyar Gombe ta tsakiya, Injiniya Musa Gwani Bimason da mataimakin ma’ajin jam’iyyar PDP na jiha, Muhammad Yusuf Pindiga sun sauya sheka zuwa jam’iyyar NNPP kwanakin baya.
Sauran wadanda suka sauya sheka a kwanakin baya sun hada da; Hon. Rambi Ayala da Hon Hamza, membobi masu wakiltar Billiri Gabas da Funakaye ta Kudu.
Shugabannin matan PDP na karamar hukumar Gombe da Dukku, Maryam Muhammad Audi da Asabe Saleh suma sun fice daga PDP sun koma NNPP.
A wani labarin kuma,Da Duminsa: Okupe Ya Tabbatar Da Sakinsa Daga Hannun EFCC
An saki tsohon Darakta-Janar na kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa na Jam’iyyar Labour Party (LP), Doyin Okupe. Kamar yadda The Nation Ta ruwaito.
Jami’an tsaro na farin kaya (DSS) sun kama Okupe a safiyar ranar Alhamis a filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas.