A Lokacin da wasu gwamnoni ke bayyana aniyar su ta Karin albashi a ranar ma’aikata ta bana da ta Gabata a jiya Laraba.
Gwamnan Enugu Ifeanyi Ugwuanyi, Shi kuwa cewa yayi jahar ba ta da kudin da za ta yi alkwarin Biyan Sabon Albashi duba da yadda Tattalin Arzikin jahar ke komawa baya a kasa baki daya.
Duk da na saka hannu kan kudurin amma ina fatan zaku taya mu da addu’a a kara samun hanyoyin kudin shigar jahar Tukuna, inji shi.
A Wani bangare Guda kuma Gwamnan Ebonyi, David Umahi, yace shima ba zai zama farko a masu biyan ba, sannan ba zai zama shine na karshe ba.
Ya ce Ma’aikata su shirya daukar duk wani kari da za su gani na Kudin Haraji domin ta haka ne kadai Jahohi za su iya samun Damar Biyan Karin Albashi.
Lokacin da ya ke Maida Martani ga gwamnati Kwamared Agnes Funmilayo Sessi, shugaban kwadogo na jahar legas, cewa ya yi duk Wanda ba zai iya biyan haka ba to ya ajiye mukaminsa Dan baidace yaja ragamar Jama’a ba.
Ta kara da cewa in zasu iya cire rashawa da yawan hidima ba abin da zai hana hakan yiwuwa.