A daidai lokacin da wa’adin Shugabancin Ƙungiyar Gwamnonin Najeriya ke zuwa karshe wanda Gwamnan jihar Zamfara Yari ke shugabanta, wasu daga cikin gwamnoni sun fara nuna sha’awar su da maye gurbin Gwamnan.
Wanda ke kan gaba wajen nuna sha’awar shi a neman shugabancin kungiyar shine gwamnan jihar Kaduna Nasiru Ahmad El Rufa’i.
El Rufa’i dai ya yi kaurin suna wajen kafiya da tsauri gami da jajircewa a tsakanin sauran takwarorin shi, inda ake ganin idan ya zama shugaban kungiyar Gwamnonin zai haifar da wani sauyi na musamman.