Kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan dake kasar Italiya ta sanya kafa ta yi fatali da tayin pam miliyan 85 da Chelsea ta yi kan dan wasan gabanta Romelu Lukaku.
Yanzu haka babu wanda Chelsea kw nema ido rufe din inganta yan wasan gabanta kamar Lukaku, bayan da Borussia Dortmund ta Jamus ta ce atafau ba za ta baiwa Chelsea dan wasan gabanta Erling Haaland ba.
Da ma dai Milan ta shiga wani halin masshashsharan kudi lamarin da ake ganin tilas ne ta saida Lukaku don cike lalitar ta.
Lukaku wanda tsohon dan wasan Chelsea ya nuna zakakuranci a kakakr da ta gabata inda ya taimaka wa Milan ta lashe gasar Serie A a karon farko tun shekara ta 2010.
Akwai bayanai dake nuni da cewa Chelsea za ta iya hadawa Inter Milan har da dan wasan gefen ta Marco Alonso kawai don jan ra’ayinta kan Lukaku.