Mai koyar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, Mikel Arteta ya ce ba shi da tabbacin ko zai samu kudin da zai siya sabbin ‘yan kwallo a kungiyar ta yadda za su kalubalanci abokan hamayyarsu a harkar kwallon kafa a kakar wasa mai zuwa.
Arsenal ta yi nasarar doke Liverpool daci 2-1 ranar Laraba, wacce ta lashe kofin Firimiya ta bana, sai dai Arsenal na da jan aikin samun gurbin shiga gasar Zakarun Turai ta badi wanda .
Arsenal din tana mataki na tara a kan teburi da maki 53 da tazarar maki uku tsakaninta da ta shida wato Wolverhampton sai dai an tambayi Arteta ko zai samu kudin da zai sayo ‘yan wasa a badi a hirarsa da Sky Sports ya ce ba tabbas din siyan ’yan wasan.