Daga bana Mun daina amincewa da NABTEB domin bada gurbin Karatu kai tsaye – JAMB
Hukumar Shirya Jarabawar Shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB a ranar Alhamis ta ce ba za ta sake la’akari da sakamakon A’level da hukumar kula da harkokin kasuwanci da fasaha ta kasa ta fitar ba ga masu neman shiga makarantun gaba da sakandare kai tsaye.
Magatakardar Hukumar ta JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede ne ya bayyana hakan a yayin taron tsare-tsare 2022 da ke gudana a yanzu haka a ɗakin taro na kasa da kasa da ke Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: Da Dumi-dumi: Shugaba Buhari Ya Jagoranci Taron Majalisar Tsaro Ta Kasa A Abuja
“Mai girma ministan ilimi ya amince da cewa NABTEB A’level GCE, ba za a sake amincewa da shi a matsayin bada gurbin Karatu na DE daga 2022. Don haka, duk waɗanda suka riga sun samu kafin wannan ranar za su iya amfani da shi,” cewar Oloyede
Da yake karin haske a taron tsare-tsare, Oloyede ya bayyana wasu ƙalubalen da hukumar ta fuskanta wajen gudanar da Jarabawar UTME/DE na shekarar 2022.
Ya zayyana kalubalen kamar haka; rashin aikin jarrabawa, maye gurbin Ɗalibai, masu cin hanci da rashawa na CBT masu zagon kasa, iyaye suna karfafa satar jarabawa, yaudarar jama’a ta ‘yan kungiyar, dogon bincike da gurfanar da su gaban kotu.