Babban Malami a Jahar Kano Abduljabbar Nasiru Kabara, zai sha shagalin Sallar sa a cikin gidan Maza, kamar yadda gwamnatin Jahar Kano ta sanar. Kamar yadda Jaridar Dailytrust ta wallafa a shafinta
Za a gudanar ba babbar Sallah a ranar Talata, idan Allah ya kaimu.
A wani bayani da ya fito a daren Juma’a, Malam Muhammad Garba kwamishinan yada labarai na Jahar Kano, yace Dan tamoren Malaminnan an mika shi zuwa kotu.
KARANTA:- Idan kasan kana karbar cin hanci ka ajiye aikin ka, Bawa ga jami’an EFCC
Kotun ta bada umarnin tsare shi har zuwa ashirin da takwas ga watan July, a gidan Maza.
“Sheik Abduljabbar Nasiru Kabara, Malami ne mazaunin Kano, an sansa ta tabargaza gami da munanan kalamai kan Sabban Annabi Muhammad S.A.W dama Annabin shima da kansa, an mika shi zuwa kotu kan laifin aibata Manzon Allah S A W.”
“An dai kama Abduljabbar Nasiru Kabara ne a ranar Juma’a sha shida ga watan July, inda aka mika shi zuwa babbar kotun Shari’a dake kofar kudu, Alkali Ibrahim Sarki Yola, ya tuhumi Malamin akan laifin aibata Manzon Allah S.A.W, gami da cin mutuncin sahabban Manzon Allah S.A.W.”
“Bayan an Kammala zaman kotun a ranar, an dage karar izuwa ashirin da takwas na watan July, inda za’a cigaba da tsare Malamin a hannun Yan sanda har zuwa ranar Litinin, inda daganan za’a tafi dashi gidan Maza.”
A wani labarin
Idan kasan kana karbar cin hanci ka ajiye aikin ka, Bawa ga jami’an EFCC
AbdulRaaheed Bawa shugaban hukumar EFCC ya gayama Mutanensa idan akwai mai cin hanci a cikinn su, to su gaggauta ajiye aikin su.
Ya fadi hakane lokacin da yake bayani a babban Ofishin su dake Makurdi babban birnin Jahar Benue, Bawa yace ana bukatar jajircewa da maida hankali wajan gudanar da aiki.
Ya cigaba da cewa babu yadda za’ayi mai cin hanci yace zaiyi fada da masu cin hanci.
“Bari in tunama kowannanmu wannan aiki ne na musamman, wanda gwamnati, Mutanen Najeriya da sauran kasashen ketare na sanya Ido kanmu, don ganin munyi kyakykyawan aiki.”
“Ba za mu amince da duk wani nau’in cin hanci a wannan hukumar ba, ba damuwarmu bane idan munyi aiki da mutane kadan nagartattu, kuma a shirye muke mu kori duk wanda muka kama da cin hanci, idan akwai wanda yake ganin bazaiyi abunda kasa ta daukeshi yayi ba, to yana iya ajiye aikin sa.”
Ya kuma shawarci sauran ma’aikatan dasu zage damtse wajan tabbatar da aikinsu.
Kamar yadda ya fada, “hukumar ba za ta huta ba har sai ta cimma abunda kasa ta sanya su, sannan kasashen ketare sun tabbatar da cika ayyukan su.”
Yace hukumar kuma zata cigaba da kawo cigaba ga ma’aikatanta ta hanyar salon horaswa daban-daban.
“Muna cigaba da gyara, da samarwa da kuma yin kwaskwarima ga makarantun EFCC, wannan don kawai ma’aikatanmu su samu isashshen gurin aiki, don aiwatuwar aikin da aka bukacesu dayi, sannan kuma da cimma burinkan kasa a kanmu.
Comments 1