Wani tsoho mai shekara 78 a duniya, wanda ya fito daga gundumar Bumula, a yankin Bungoma na ƙasar Kenya, yana can yana jinya bayan surikarsa ta gandara masa cizo a mazakuta yayin da suka samu saɓani.
Tsohon mai suna Vincent Barasa, matar ɗan sa ta biyu suna is Evelyn Okello, itace tayi masa wannan aika-aikar a ranar 28 ga watan Janairun 2023, yayin da yake ƙoƙarin raba su faɗa da wata ƙawarta a gidan su. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.
KU KARANTA KUMA: Tirƙashi: Bidiyon tsohon da ya kwashe shekara 65 bai yi barci ba ya janyo cece-kuce
Da yake tattaunawa da wani gidan talabijin na Citizen TV Kenya a ranar Talata 31 ga watan Janairu, Barasa yace yana cikin cin abincin sa da misalin ƙarfe huɗu na yamma, lokacin da ya jiyo hargitsi a gidan ɗan sa mai suna Godfrey Wekesa.
Ɗaya daga cikin jikokin sa ya sanar da shi cewa surikar sa na faɗa da wata wacce ta zo daga wata kasuwa ta kusa da su.
Ya gaggauta zuwa wajen domin ƙoƙarin sulhunta su amma sai suka ƙi bari, kawai sai ya yanke shawarar ya tafi ya kyale su.
Yana juya baya kawai sai Evelyn ta biyo shi ta kwaɗa masa dutse. Nan take ya zuɓe ƙasa wanwar sannan ta hau ruwan cikinsa tana cizon ƙirjin sa.
Tsohon yayi ƙoƙarin tureta daga jikinsa amma ya kasa inda daga bisani ta gandara masa cizo a mazakutar sa.
“A yayin da na juya ina tafiya, kamar taji haushi sai ta jefo min dutse inda ta sameni a ƙeya. Daga nan ta cije ni a mazakuta.” A cewar sa.
Bayan aukuwar lamarin, fusatattun mutanen da suka zo wajen sun lakaɗawa matar dukan tsiya kafin suka ɗauki tsohon zuwa duba lafiyar sa.
Wekesa ya bayyana cewa matar sa ta cika rigima sannan har barazanar halaka shi tare da ɗiyar sa ta sha yi a baya.
A halin da ake ciki, ƴan sanda na neman wacce ake zargin ruwa a jallo bayan an nemeta an rasa.
Yadda Wata Matar Aure Ta Aika Surikarta Barzahu Kan Naman Miya
A wani labarin na daban kuma, wata matar aure tare da taimakon ɗanta, ta halaka surikarta.
An tura wata matar aure mai suna Charity Upev, ƴar shekara 40 a duniya, tare da ɗanta mai suna Tertsea, gidan gyaran hali a jihar Benuwai bisa zargin lakaɗawa surikarta mai sunan Fanen, dukan tsiya wanda yayi sanadiyyar mutuwarta saboda nama.